Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Ya Taimaka Wajen Kashe Mahaifinsa


Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta nunawa taron manema labarai wasu masu aikata manyan laifuka, ciki har da wani matashi da aka hada kai da shi aka sace mahaifinsa

Shi dai matashin mai suna Isa Ibrahim, mai shekaru 20 da haihuwa ya hada kai da wasu masu satar mutane suka sace mahaifinsa Ibrahim Adamu, mai shekaru 50, suka kuma kashe shi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Osun, Mista Olafimihan Adeoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa, Isa dake zaman da ga mutumin da aka kashe shine ya hada baki da masu satar mutane suka sace shi suka kuma kashe shi, tare da jefa gawarsa cikin kogi.

Haka kuma rundunar ‘yan sandan ta nuna wasu mutane biyu da ake zargin sune suka sace tare da kashe Ibrahim Adamu, bayan da suka karbi kudi har Naira Miliyan Uku kafin su kashe shi.

Bincike dai ya nuna cewa shi dai Isa Ibrahim, ya kulla yarjejeniya da masu satar mutanen da cewa idan komai ya tafi dai-dai zasu bashi Naira Dubu 500, amma daga bisani bayan sun sami kudin sai suka bashi Naira Dubu 45 kacal.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Hassan Umaru Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG