Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Mummunan Hadarin Jirgin Kasa Ya Auku A Kamaru


"Son zəng" - Kyiv, Ukrayna
"Son zəng" - Kyiv, Ukrayna

Rahoto da muka samu da dumiduminsa na cewa wani jirgin kasa shake da mutane dake kan hanyarsa tsakanin biranen Yaunde da Douala ya samu mummunan hadari kuma mutane fiye da dari sun rasa rayukansu

Da misslin karfe hudu na rana jirgin kasan da ya taso daga babban birnin kasar Yaunde da taragu goma sha shida kuma yana kan tafiya wasu taragun suka kama da wuta.

Duk da wutar da ta kama jirgin ya cigaba da tafiya har tsawon kusan kilomita dari kafin taragu shida su fada cikin wani kwazazzabo. Nan take an samu gawarwakin mutane fiye da dari.

Baicin gawarwakin da aka samu akwai mutane kimanin dari biyu da hamsin suna asibiti saboda raunuka da suka samu. Ana kuma cikin zakulo gawarwakin da taragun suka danne.

Ministocin sufuri da na kiwon lafiya sun ziyarci wurin da jirgi mai saukan ungulu. Shi ma Firayim ministan kasar ya kira taron gaggawa saboda shugaban kasar baya nan kuma babu wanda ya san inda yake.

Ga tattaunawa da Garba Lawal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:47 0:00

XS
SM
MD
LG