Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sojan Afghanistan Ya Bindige Sojojin Amurka


Kungiyuar Taliban tace mutumen da ya harbe sojojin Amurka har lahira mayakin ta ne

Hukumomin kasar Afghanistan sunce daya daga cikin sojansu ya bindige sojoji biyu na Amurka har lahira, kuma ya raunana wasu biyu a gabascin Afghanistan din.

A yau Assabar ne wannan al’amarin ya faru a gundumar Achin dake lardin Nangarhar, kuma nan take sauran sojan Amurka su ma suka bindige mutumen, kamar yadda kakakin gwamnati Attaullah Khogyani ya gayawa VOA.

Wani mai magana da yawun rundunar sojan Amurka da aka tuntuba kan lamarin ya tabattarda cewa suna sane da “abkuwar wani al’amari da ya faru a gabascin Afghanistan” kuma zasu bada “karin bayani da zaran lokacin hakan yayi.”

Haka kuma wani kakakin kungiyar Taliban yace sune suka cinna ta’asar, inda yace mutumen da ya harbe sojan na Amurka mayakin su ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG