Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Ya Farma 'Yan Makarantar Firamare Da Sara


Da safiyar yau wani ya shiga makarantar firamare a Jabi kusa da Maiduguri ya dinga sara kan mai uwa da wabi kan daliban.

Wani da ba'a tantance ba ya shiga makarantar firamaren Jabi kusa da Maiduguri, cikin jihar Borno, inda ya fara saran daibai da adda.

Lamarin ya yi sanadiyar mutuwar dalibai biyu nan take da kuma rufe makarantar garin yadda daliban suka fice a kidime yayinda wasu daga ciki suka samu raunuka daga saran addar.

Sai dai rahotanni sun ce tuni ma'aikatan makarantar suka yi kukan kura suka damke mutumin wanda yake rike da addar, an bayya cewa ya sari daya daga cikin malaman makarantar.

Wani ganau da ya zanta da wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, ya ce mutumin ya fito ne daga gefen garin ta kofar baya rike da adda. Kafin a ankara ya shiga aji. Malamar dake koyaswa da ta daga hannunta sai ya sareta.

Ba'a iya tantance ko yara nawa suka ji rauni ba sanadiyar saran saboda yawancinsu sun arce daga makarantar da rauni.

Mutumin da ya kai harin ba mazaunin wurin ba ne sai dai tunda yana hannun jami'an tsaro za'a san inda ya fito da kuma manufarsa.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG