Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Ya Tunkari Fadar White House Da Ikirarin Cewa Yana Dauke Da Bom


Jami’an tsaron shugaban Amurka sun kara karfafa tsaro sakamakon yunkurin da wani mutum ya tuka mota har izuwa inda ake duban tsaro a Fadar White House a yammacin jiya Asabar inda yace yana dauke ne da Bom.

Jami’ai sunce nan take aka kame mutumin sannan aka kwace motar.

Mai Magana da yawun jami’an tsaron yace an fara gudanar da binciken lamarin. Ba a tabbatar da ko akwai Bom din da ya ambata a cikin motar ba.

Shugaba Donald Trump baya cikin fadar ta White House a lokacin da wannan abu ya faru. Yana Katafaren gidansa dake Mar-a-Lago dake Florida domin hutun karshen mako, wannan shine hutun karshen mako na Biyar da ya yi a Gidan tun hawansa mulki a ranar 20 ga watan Janairu.

Al’amarin ya faru ne awanni bayan Jami’an tsaron sun damke wani da ya tsallaka cikin harabar ta White House ta wurin da ake ajiye kekune.

Rahotanni sun ce Jami’an tsaron na farin kaya sun cafke shi nan da ann cikin mintuna biyu.

Kararrawar gargadi tayi ta kara a White House din a lokacin da aka samu kutsen wacce ta jawo Jami’ai da manya manyan bindigogi suka fito da gudu harabar gidan domin kare afkuwar hakan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG