Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Ya Wurga Bam Na Iskar Gas A Gidan Shugabar Kasar Mynmar Aung San Suu Kyi


Mai magana da yawun shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi, ya bayyana cewa, a yau Alhamis wani ya wurga bam mai cike da iskar gas a gidanta da ke gefen rafi a birnin Yangon.

Mai magana da yawun shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi, ya bayyana cewa, a yau Alhamis wani ya wurga bam mai cike da iskar gas a gidanta da ke gefen rafi a birnin Yangon.

Zaw Htay ya ce Suu Kyi wacce ke da lambar yabo ta Nobel, tana babban birnin kasar na Naypyitaw a lokacin da al’amarin ya faru.

Ya kara da cewa, bam din ya yi barna amman ba mai yawa ba ga gidan na ta.

Gidan da ke gefen rafin, shi ne wanda Suu Kyi ta yi zaman daurin talala na tsawon mafi aksarin shekaru 20 a karashin mulkin sojin kasar, abin da ya janyo mata kima a idon duniya har ana ganin ta a matsayin jigo ga mulkin dimukradiyya.

Amman abin da ake gani a duniya game da yadda ta nuna halin ko in kula akan rikice-rikicen da ke shafar al'ummar da ta kunshi Musulmai 'yan kabilar Rohingya ya zubar mata da kima.

Kusan ‘yan Rohingya 700,000 ne suka bar gidajensu zuwa Bangladesh tun watan Agustan da ya gabata domin gujewa murkushe sun da jam'ian tsaron Myanmar ke yi. Shaidun ‘yan Rohingya da masu fafutukar 'yancin bil'adama sun zargi sojojin kasar da aikata kisan kai, fyade da kone-kone a wani yunkuri da majalisar dinkin duniya da Amurka suka ce na kare dangi ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG