Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Yaro Dan Asalin Najeriya Ya Ba Duniyar Dara Mamaki


Wasu yara masu darar Chess

A cigaba da bayar da mamaki da 'yan Najeriya ke yi a fannoni daban-daban na rayuwa a fadin duniya, wani yaro dan asalin Najeriya mai shekaru 8 ya zama zakara a gasar da aka yi a birnin New York na nan Amurka

Wani yaro mai shekaru 8 dan asalin Najeriya, wanda ke gudun hijira tare da iyayensa a birnin New York da ke nan Amurka, ya lashe gasar wasan dara ta zamani ko kuma Chess a turance.

A makon da ya gabata, aka ayyana Tanitoluwa Adewumi, a matsayin wanda ya lashe gasar a birnin New York, wacce aka yi a matakin ‘yan makarantar Nursery zuwa ‘yan aji uku na Firaimare.

Tani, kamar yadda aka fi kiransa, na zauna ne a wani sansanin ‘yan gudun hijira tare da iyayensa a yankin Manhattan a New York.

Ana sa ran nan gaba, Tani zai kara a gasar kasa ta ‘yan makarantun firaimare da za a yi a watan Mayu.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG