Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wariyar Launin Fata: An Yi Ca Akan Gwamnan Virginia Kan Wani Hoto


Gwamnan jihar Virginia, Ralph Northam, yayin da yake shirin gabatar da wani taron manema labarai a birnin Richmond, ranar 31 ga watan Janairu, 2019.

Hoton dai ya nuna wasu mutane biyu, daya ya mulka wani bakin penti a fuskarsa, dayan kuma ya rufe fuskarsar da irin fararen kayannan mai rufe fuska, wanda ‘yan kungiyar KKK masu fafutukar ganin an fifita farar fata, ke sakawa.

Kiraye-kirayen da ake yi na neman gwamnan jihar Virginia ya sauka daga mukaminsa, na ci gaba da karuwa, bayan bullar wani hotonsa wanda ke nuna wariyar launin fata, wanda ya dauka a lokacin yana makarantar koyon aikin likitanci shekaru 30 da suka gabata.

A jiya Juma’a Ralph Northam ya fito ya nemi afuwa, kan fitowa a wani kundin hoton dalibai da aka dauka a shekarar 1984, wanda ke nuna izgilanci ga bakaken fata.

A wani jawabi da ya yi ta kafar bidiyo, Northam ya ce wannan hoto, ba yana nufin haka ra’ayinsa yake a yanzu ba.

Ya kara da cewa, babu yadda zai iya janye wannan abu da ya riga ya faru, ba zai kuma iya kawar da irin illar da dabi’arsa ta haifar a yau ba, amma a shirye yake ya dauki alhakin wannan abu mara dadi, domin sake neman yardar jama’a.

Hoton dai ya nuna wasu mutane biyu, daya ya mulka wani bakin penti a fuskarsa, dayan kuma ya rufe fuskarsar da irin fararen kayannan mai rufe fuska, wanda ‘yan kungiyar KKK masu fafutukar ganin an fifita farar fata, ke sakawa.

Gwamnan na jihar ta Virginia, ya tabattar da cewa lallai yana cikin hoton, amma bai bayyana ko shi ne wanne a cikin mutanen biyu ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG