Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Alkalai a Sudan Ta Kudu Sun Nemi a Maida Su Bakin Aiki


Wani tsohon Alkalin Sudan ta Kudu ya ce, ya kamata a mayar da shi da sauran alkalai 14 bakin aikin su, nan da nan, bayan da wata kotu a gabashin Afirka ta yanke hukuncin cewa, Shugaba Salva Kiir ya kore su ba bisa ka’ida ba shekaru uku da suka gabata.

Tsohon Alkalin Kotun daukaka kara a Sudan ta Kudu, Malek Mathiang Malek, ya ce, ya na godiya ga Kotun Afirka ta Tsakiya da ta yanke masu wannan hukunci. Shugaba Kiir ya kori Malek da abokan aikinsa su 14 a shekara 2017 bayan da suka shiga yajin aiki don neman ingancin yanayin aiki.

"Ta yi mini adalci ba wai ni kadai ba har ma da sauran alkalan Sudan ta kudu, wadanda aka kore su da kuma ... dukkanin ‘yan Sudan ta Kudu, saboda kun san, cewa Sudan ta Kudu abu daya take nema, bin doka da oda," kamar yadda Malek ya shaidawa shirin “South Sudan In Focus” na Muryar Amurka.

Malek ya ce, an tilasta masa ne neman adalci a wajen kasar, tun lokacin da shugaban Sudan ta Kudu ya aiwatar da wannan doka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG