Accessibility links

Wasu Ba Su Gane Taron Kasa Ba Inji Kungiyar Matasa

  • Halima Djimrao

Wata mata rike da tulin tutocin Najeriya.

Kungiyar matasan arewa ta Northern Youth Progressive tace masu kiran a raba kasa gida biyu ba su fahimci abun da ake nufi da taron kasa ba

Wata kungiyar matasan arewa da ake kira Northern Youth Progressive da Turanci tace bahaguwar fahimtar da wasu 'yan Najeriya suka yiwa taron kasar da ake shirin yi a Najeriya ita ce dalilin su na cewa a raba Najeriyar gida biyu. Wakilin Sashen Hausa a Kaduna, Isah Lawal Ikara, ya ce shugaban kungiyar matasan ta Northern Youth Progressive, Barrister Abubakar Aminu Kurawa ya yiwa manema labarai bayani a garin na Kaduna inda ya shaida mu su cewa haramun ne a doka ma wani dan kasar yayi kiran cewa a raba Najeriya gida biyu.

XS
SM
MD
LG