Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu da Ake Zaton 'Yan Boko Haram Ne Sun Kai Hari Damaturu a Jihar Yobe


Alhaji Ibrahim Geidam gwamnan jihar Yobe

Wasu ‘yan kunar bakin wake sun kai hari birnin Damaturu a arewa maso gabashin Nigeriya suka kashe akalla mutane 15.

Hukumar bada taimakon gaggawa da ake kira NEMA a takaice tace, ‘yan kunar bakin wake guda 3 ne suka dana tada bama-baman a cikin garin Damaturu dake jihar Yobe.

Shedun gani da ido sun tabbatar da cewa, daya daga harin sassafen ya tashi ne a kusa da wani masallaci make da jama’a suna sallah.

Wani bam din kuma ya sake tashi a wasu rukunin gidajen da ake ginawa. Mutane da dama aka kwasa zuwa asibiti bisa raunin da suka samu.

Ba dai wanda ya dau alhakin kai harin, amma can baya mayakan ‘yan Boko Haram sun sha kai hare hare a yankin.

A ranar Lahadin da ta gabata ma kungiyar ta dauki alhakin kai harin da aka yi a wasu garuruwa biyu dake kewaye da Abuja, baban birnin tarayyar Najeriya har mutane 15 suka mutu.

XS
SM
MD
LG