Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Fasinjan Jirgin Ruwan Shakatawa Sun Tsallake Rijiya Da Baya


Wasu fasinja suna jira a kwashe su daag jirgin na Viking Sky, Maris 23, 2019.

Ma’aikatan Viking Sky sun aika da yakuwar neman taimako a ranar Asabar lokacin da injin din jirgin ya lalace.

Masu ceto sun yi amfani da jiragen sama masu saukar ungulu suka kwashe mutum 479 daga jirgin ruwan da ya lalace a can yammacin gabar tekun Norway kafin a sake ta da injin jirgin a jiya Lahadi.

Mutum 29 suka samu raunuka a cikin rudanin da ya biyo bayan matsalar da jirgin ruwan yawon bude ido na Viking Sky ya samu lokacin da ya yi ta tangadi cikin igiyar ruwa mai karfi.

Kungiyar ba da agajin gaggawa ta Norwagian Red Cross ta ce wadanda suka samu raunuka sun samu karayane a kashinsu da kuma yankewa.

Ma’aikatan Viking Sky sun aika da yakuwar neman taimako a ranar Asabar lokacin da injin din jirgin ya lalace.

A lokacin da lamarin ya faru, jirgin ya doshi wasu duwatsu da karkashin ruwa inda nisansu bai fi mita 100 ba.

.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG