Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Hotuna Sun Sake Dagula Rikicin Da Ake Yi Kan Kogin Nilu


Hotunan tauraron dan adam na gina madatsar ruwa da kasar Ethiopia ke yi a Kogin Nilu MAXAR TECHNOLOGIES/ASSOCIATED PRESS

Yayin da ake neman bakin zaren yadda za a sasanta rikicin aikin gina madatsar ruwan da kasar Ethiopia ke yi a Kogin Nilu, wasu hotuna da suka nuna an fara aikin sun janyo tsaiko a kokarin shawo kan takaddamar tsakanin kasar ta Habasha, Masar da Sudan.

Wasu sabbin hotunan tauraron dan adam da hukumar da ke binciken sararin samaniya ta nahiyar turai ta dauka a makon da ya gabata, sun nuna cewa kasar Ethiopia ta fara aikin cike madatsar ruwan nan a Kogin Nilu.

Bayyanar hotunan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ta da jijiyar wuya kan shirin gina dam din wanda tattaunawar da ake yi tsakanin Masar, Ethiopia da Sudan ta sarkafe.

Sai dai hukumomion kasar ta Ethiopia sun musanta wannan ikrari, amma sun ce suna kan bakarsu ta aiwatar da aikin gina madatsar ruwan nan gaba a cikin wannan wata, aikin da aka kwashe shekaru ana yi.

Akalla dala biliyan 4.5 wannan katafaren dam da Ethiopian ke ginawa ya ci, idan kuma aka kammala shi, zai zamanto madatsar ruwan samar da wutar lantarki mafi girma a duk fadin nahiyar Afirka, wanda zai iya ba da wuta mai karfin ma’aunin gigawattrs 6.4.

Sai dai aikin wanda ya sa sauran kasashen da ke da iko da Kogin wato Masar da Sudan sun shiga fargabar zai iya shafar amfanin da suke samu daga Kogin – domin a cewarsu daga nan suke samun ruwan da suke amfanin da shi a Yau da kullum.

Ita dai Masar ta ce kashi 90 na ruwan da take amfani da shi a kasarta daga Kogin na Nilu take samu

A halin da ake ciki, yunkurin da kasashen ke yi na sasanta rikicin ya cije a wuri guda ba tare da an samu matsaya ba.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG