Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Jami'an Ma'aikatar Sufuri A Nijar Sun Fara Yajin Aikin Gargadi


Kungiyar
Kungiyar

A jamhuriyar Nijar, jami’ai a ofishin Ministan sufuri sun fara yajin aikin kwanaki biyu yau alhamis, da nufin nunawa hukumomi rashin aminta da wasu kwangilolin da suke zargin an bayar cikin wani yanayi mai duhu.

Kwangilar buga lasisin tuki da aka ba wani kamfanin kasar waje ba tare da fayyacewa ‘yan kasa zahirin abubuwan da wannan yarjejeniyar ta kunsa ba, ita ce ta harzuka wadannan ma’aikata a wani lokaci da ayyukan harhada takardun ababen hawa da na buga lambobin motoci suka koma hannun wani kamfanin kasar waje, mafarin wannan yajin aikin kenan na tsawon kwanaki biyu, inji sakataren yada labaran kungiyar SYNPAT Oumarou Moussa.

Sai dai hukumomi na cewa babu kamshin gaskiya akan dukkan abubuwan da wadannan ma’aikatan ke korafi akansu.

Diallo Amadou ISSIFI, shine daraktan ofishin ministan sufurin, yace sun shafe wunin shekaranjiya Talata su na tattaunawa kuma sun sami fahimtar juna akan koke-koke 11 daga cikin 12 da ma’aikatan suka gabatar. Abinda ba su fahimci juna akansa ba shine batun takardun yarjejeniyar da suka bukaci a basu, kuma wannan doka ba ta yarda a baiwa kowa takardar yarjejeniyar ba har sai an wallafa ta a ma’ajiyar takardun hukuma da ake kira journal official da turanci. Yanzu haka ana cikin sake duba wannan yarjejeniya domin yi mata gyaran fuskar da za ta yi daidai da bukatun ‘yan kasa. Saboda haka rashin fahimtar dake tsakanin gwamnati da ma’aikatan ba ta kai inda za a jingine aiki ba amma ko gobe a shirye muke a sake bude tattaunawar, a cewar Diallo.

Wadannan jami’ai sun lashi takobin ci gaba da gwagwarmaya har sai hakarsu ta cimma ruwa saboda haka kungiyarsu ta fara hangen shiga wani yajin aikin a makon gobe muddin basu ji wata amsa mai gamsarwa ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG