Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Jihohi Za Su Koma Aiki a Mako Mai Zuwa – Trump


Shugaban Amurka Donald Trump (AP Photo/Patrick Semansky)

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, a mako mai zuwa wasu jihohin kasar za su bude harkokin kasuwancinsu tare da bin ka’idojin kare yaduwar cutar coronavirus.

Trump ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wani taron manama labarai da aka yi a Fadar gwamnati ta White House.

Jihohin Texas da Vermont za su koma harkokinsu na yau da kullum a ranar Litinin, yayin da Montana za ta koma a ranar Juma’a, a cewar Trump.

“Muna ci gaba da ganin alamu da ke nuna cewa cutar ta wuce shallin da take kamari, sannan ayyukan gwaje-gwajen da muke yi na kara inganta.”

Sai dai Trump din bai nuna wata shedar hakan ba.

Sai dai gwamnonin wasu jihohi sun yi gargadin cewa, su ba za su yi garajen bude harkokin kasuwancinsu ba, har sai an samu karin ayyukan gwaje-gwaje – gudun kada su kara yaduwar cutar

Akwai dai daruruwan mutane da suka yi zanga zanga a biranen Amurka da dama kan matakan da aka saka na dakile yaduwar cutar.

Korafinsu shi ne yadda matakan suke shafar harkokin tattalin arzikin Amurka Idan aka yi la’akkari da yadda aka umurci mutane su zauna a gida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG