WASHINGTON D C —
Kungiyar Hezbollah ta ce wasu jiragen saman Isra’ila marasa matuki guda biyu sun fado a Lebanon a cikin dare.
Jirgi na biyu ya fada akan wani gini inda cibiyar yada labaran ‘yan Hezbollah ta ke a unguwar Dahyeh dake Beirut, babban birnin Lebanon.
Mai magana da yawun kungiyar ta Hezbollah, Mohammed Afif, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa, ba su suka harbo jirgin mara matuki ba.
Ya zuwa yanzu dai Isra’ila ba ta ce uffan ba game da faduwar jiragen.
Firayin ministan Isra’ila Saad Hariri ya bayyana faduwar jiragen biyu a matsayin saba doka da tsokana akan Lebanon da kuma barazana ga zaman lafiyar yankin.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 31, 2023
Fafaroma Francis Ya Kai Sakon Zaman Lafiya A Afirka Ta Tsakiya
-
Janairu 30, 2023
Mutane 88 Sun Mutu A Wani Harin Bomb A Pakistan
-
Janairu 18, 2023
Mataimakin Shugaban Gambia, Badara Alieu Joof Ya Rasu A India
Facebook Forum