Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kamfunan Sadarwan Najeriya Na Cutar Al'umma Da Gwamnatin Najeriya


Buhari Saraki, shugaban majalisar dattawan Najeriya , majalisar da ya kamata ta kafa dokar kare kasa daga magudin kamfanonin sadarwa

Muryar Amurka ta bi sawun yadda wasu kamfanonin sadarwa ke yiwa Najeriya magudi wajen karkata kira daga waje ya zo tamkar daga kasar aka yi lamarin dake basu damar biyan gwamnati N4 kowane kiran maimakon N24

Kusan shekaru 17 aka fara anfani da wayar salula a Najeriya wadda ta taimaka gaya wajen ingata zamantakewa da samar da ayyukan yi da kuma samar wa kasa makudan kudaden shiga.

Amma a 'yan kwanakin nan wasu kamfanonin sadarwan sun fara yiwa kasar coge tana asarar miliyoyin kudi. Misali, idan an kira mutum daga kasar waje maimakon ya ga lambar wajen sai ya ga ta Najeriya.

Muhammad Sani Abubakar wani dan jarida dake aiki da wani gidan radiyon kasar waje ya yi tsokaci akan al'amarin. Ya ce sau tari idan yana aiki da zara ya ga lambar Najeriya ba zai dauka ba sai an tura masa sakon email daga ofishinsu dake kasar waje su tambayeshi dalilin da ya sa baya daukan kira. A lokacin ne zai farga cewa kiran daga waje ne amma yana shigowa da lambar Najeriya.

Lamarin ya sa ana zargin kamfanonin da yin muna-muna wajen samar da kudaden shiga kan kowane dakika da aka kira. Misali kowane kira na minti daya daga kasar waje ana biyan N24 ne wa gwamnati sabanin N4 kan kiran cikin gida.

Binciken Muryar Amurka ya nuna cewa wasu kamfanoni suna zuba N20 a aljihunsu ne kana su biya gwamnati N4 kan kiran da ya fito daga ketare.

Akan haka Muryar Amurka ta je ofishin MTN (Mobile Telephone Nigeria) daya cikin manyan sadarwa na kasa. Awal Abdullahi wanda ya kasance shugaban kamfanin shiyar arewa ya tabbatar suna da masaniya da lamarin. Injishi wasu bata gari ne da suke da naurar da zasu tare kira daga waje su idar dashi da lambar cikin gida. Injishi abu ne da ya addabesu kuma sun kai kuka wurin hukumar dake kula dasu wato, NCC. Hukumar tana kokari kuma duk wanda aka kama ana hukumtawa.

Farfesa Umar Garba Danbatta shugaban hukumar NCC ya yiwa Muryar Amurka bayani. Ya ce suna da masaniya akan abun dake faruwa kuma sun yi bincike domin daukan mataki na shari'ah. Sun samo masu aika aikar kuma sun tsayar da lasisinsu. Injishi aika aikar na kawowa kasa barazanar tsaro.

A wani bangaren Sanata Abdullahi Adamu ya ce akwai abun dubawa. Ya ce babu shakka ana cutar Najeriya wajen kudaden shiga. Ya ce a basu dan lokaci kadan zasu yi doka.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:31 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG