Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Karin Jami'an Gwamnatin Sudan Ta Kudu Sun Kamu Da COVID-19


Mai Magana da yawun gwamnatin Sudan ta kudu Michael Makuei da sauran dukan mambobin kwamitin da ke sa ido akan annobar cutar COVID-19 su 15 sun kamu da cutar wadda coronavirus ke haifarwa.

A ranar Litinin din da ta gabata ne mataimakin shugaban kasa na farko a Sudan ta kudu Riek Machar ya bayyana cewa shi da matarsa, Angelina Teny, minister tsaron kasar sun kamu da cutar coronavirus bayan da aka tilasta wa mambobin kwamitin na coronavirus yin gwajin cutar.

Makuei ya ce mambobin kwamitin sun kamu da cutar ne a lokacin da suka gudanar da wasu tarurruka lokuta da dama a babban birnin kasar.

A wani lamari na daban kuma, sama da mutum 200 aka kashe akalla wasu su 300 kuma suka jikkata a rikicin kabilancin da ya faru a makon da ya gabata a jihar Jonglei da ke Sudan ta kudu, a cewar shugabannin yankin.

Jami’ai a yankin sun ce wasu matasa dauke da makamai da ake kyautata zaton daga babban birnin Pibor suka fito ne suka kai farmakin a kauyuka hudu a ranakun Asabar da Lahadi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG