Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kasashe 8 Na Duniya Zasu Fuskaci Matsalar Shigowa Amurka


USA--New York/Televised debate between the presidential candidates of the Democratic and Republican Party Hillary Clinton and Donald Trump, Donald Trump/video grab
USA--New York/Televised debate between the presidential candidates of the Democratic and Republican Party Hillary Clinton and Donald Trump, Donald Trump/video grab

Yanzu haka kasashen Chadi,Iran,Libya,Koriya ta Arewa,Sauran suneSomaliya,Venezuela da Yemen zasu fuskanci tsauraran sharudda kafin a bari su shigo Amurka.

Masu bukatar zuwa Amurka daga wasu kasashe 8 za su fuskanci wasu sabbin tsauraran sharudda a karkashi umurnin nan na haramta ma 'yan wasu kasashe zuwa Amurka, wanda aka yi ma garanbawul wanda kuma Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya ma hannu.

Sabon umurnin, wanda zai fara aiki ran 18 ga watan Oktoba, ya shafi 'yan kasashen Chadi da Iran da Libiya da Koriya Ta Arewa da Somaliya da Siriya da Venezuela da kuma Yemen.

Jami'an gwamnatin Amurka sun ce wadannan kasashen sun ki su yi musanyar bayanai da Amurka kan batun ta'addanci da sauran batutuwa.

Sanarwar ta daren jiya Lahadi ta zo ne a yayin da wa'adin umurnin da Trump ya bayar kan wasu kasashen Musulmi 6 ke karewa, kwanaki 90 bayan da ya fara aiki. Umurnin farko ya haramta ma 'yan kasashen Iran da Libiya da Somaliya da Sudan da Yemen zuwa Amurka sai ko idan akwai wata "muhimmiyar hulda tsakaninsu da wani mutum ko abu a nan Amurka"

Nan da nan martani ya biyo bayan umurnin na Shugaban kasa, kama daga kan kungiyoyin rajin kare hakkin dan adam zuwa sauran kungiyoyin da ke ayyukan taimaka ma 'yan gudun hijira, kuma akasarin martanin na suka ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG