Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mahara Biyu Sun Kashe Mutum 29 a Amurka


A wani zub da jini na tsawon sa’o’I 13 a Amurka, wasu mahara biyu a wurare daban daban, sun kashe mutane 29 kana suka jikata wasu da dama, yayin da hukumomi ke binciken musabbabin wadannan munanan hare hare.

Shugaban Amurka Donald Trump, a jiya Lahadi, ya bukaci a sauke tutocin kasa a gine-ginen gwamnati har kwanaki biyar, domin nuna alhini da kuma alamar mutunta wadanda harbe harben ya rusa da su a El Paso da ke Texas da kuma Dayton dake jihar Ohio.

Tsana ba ta da muhallai a cikin kasarmu, inji Trump a jiya Lahadi, yayin da ya ke magana da manema labarai, ya ce ana kokarin kare faruwar irin haka nan gaba.

Ya alakanta kashe kashen da tabuwar hankali, ya kuma ce da safiyar yau Litinin zai yi cikakken jawabi a kan kashe kashen.

Trump ya ce kasarmu tana taya wadanda suka rasa ‘yan uwa da abokan arziki a cikin harbe harben jimami da bakin ciki da kuma damuwa da wadanda suka ji rauni ke ciki sakamakon wannan hare haren rashin hankali.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG