Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mahara Sun Kashe Mutum 14 a Jihar Kogi


Wasu bindigogi

Wasu mahara dauke da manyan bindigogi sun kai harin da ya hallaka mutane 14 a kauyen Agudu da ke yankin karamar hukumar Kotonkarfe ta jihar Kogi a Nigeria.

Bayanai sun nuna cewa mutane 13 daga cikin mutane 14 da aka kashe sun fito ne daga iyali guda. Bayan wadanda suka mutu akwai wasu mutane da dama da aka garzaya da su asibiti sakamakon samun munanan raunuka a jikinsu

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa Muryar Amurka cewa maharan da ba a san ko su wanene ba, sun yi amfani da makamai dabam daban wajan kai harin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da aukuwar lamarin. Kakakin ‘yan sandan jihar ta DSP Williams Aya, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi ya ziyarci yankin kuma an kara tura jami’an tsaro, ko da ya ke ya ce basu kama kowa ba tukun amma suna gudanar da bincike.

Wannan hari dai tamkar wata matashiya ce ga hukumomin jihar ta Kogi game da bukatar kara daukar matakan tsaro a yankin, musamman a daidai lokacin da al’ummar musulmi ke ci gaba da hada-hadar Babbar Sallah,

Saurari cikakken rahoton. Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG