Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Jami'an Sojin Najeriya 26 Sun Kamu Da COVID-19


Biyo bayan rasuwar wani babban Janar na rundunar sojan Najeriya da ya halarci wani taro, gwaji ya nuna an sami karin wasu manyan hafsoshin kasar da suka kamu da cutar COVID-19.

Sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta tura wa Muryar Amurka, ta nuna cewa an yi wa wasu manyan hafsoshin sojan kasa da suka halarci wani babban taronsu su dari hudu da goma sha bakwai gwajin cutar.

A cewar Kanal Sagir Musa mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya, sakamakon gwajin ya nuna cewa kimanin hafsoshi ashirin da shida ne suka kamu da cutar, wadanda dukkanninsu an killacesu bisa ka'idoji da sharuddan yaki da cutar.

Kwayar cutar COVID-19
Kwayar cutar COVID-19

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Muryar Amurka cewa cikin wadanda suka harbu da cutar har da wasu masu mukamin Janar su goma sha takwas.

A halin da ake ciki yanzu, ana ci gaba da gwajin cutar ta coronavirus ga dukkan hafsoshi da sojojin da ke aiki a shelkwatar sojin kasa ta Najeriya, a gefe guda kuma an yi feshin sinadarin kashe kwayoyin cuta a baki dayan ginin shelkwatar dakarun.

XS
SM
MD
LG