Yayin da ake ci gaba da aikin rijiistar sunayen masu zabe a shiyoyin da suka rage a Nijer, da suka hada da shiya ta hudu da ta biyar na da'irar Damagaram, wani hargitsi ya faru tsakanin wasu 'yan siyasa a wata rumfar rijista a unguwar N'Wala a shiya ta hudu.
Wani wakilin kungiyar farar hula mai sa ido kan harkokin rijistar da ya so a sakaya sunansa, ya ce ya gano wasu da ba su da takardu da aka kawo daga kauye za su yi rijista, mafarin rikicin ke nan wanda ya kai har gaban 'yan sanda, wakilin ya kuma ce yana da hujja don ya tuhumi wasu da suka shaida cewa ba su da takarda.
Mai unguwar N'Wala, Mutari Abashe ya ce sune ke bada shaida ga marasa takardu amma na unguwar su, yayin da shi kuma shugaban rumfar rijista ta N'Wala ya ce 'yan siyasa ne ke neman izgili amma su daidai suke aikin su ba wata matsala.
A nashi bayanin, Abubakar Alhaji Idandan, mai sa ido akan harkokin rijistar ya ce doka ta ce dan wata shiyar da bai samu damar yin rijista a unguwar su ba zai iya yi a wata shiyar kuma a nan ne zai yi zaben.
Ga rahoton cikin sauti.