Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Masu Cutar Ebola Sun Gudu Daga Asibiti a Congo


Wasu mutane biyu dake dauke da cutar Ebola sun gudu daga asibitin da aka killace su a Kasar Jamhuriyyar Demokradiyar Congo don halartar wani taron addu’a, ana fargabar cewa mai yiyuwa sun harbi akalla mutane hamsin da suka yi cudanya da su a wurin taron.

Wannan ya nuna karancin rashin wayarwa da jama’a kai akan yadda cutar ke yaduwa a saboda haka gwamnati da sauran yan agaji suna kara kaimi wajen wayar ma da al’umma kai don magance barkewar cutar Ebola, wacce ya zuwa jiya Alhamis ta kama mutane 52, har sun fara zazzabi.Daga cikin 52, an tabbatar da 31 sun kamu da Ebola, 13 kuma zato ake yi yayinda 8 kuma ake cewa zata iya yiyuwa su ma sun kamu amma tabbaci.

A halin yanzu kuma, Hukumar lafiya ta Kasar Jamhuriyyar Demokradiyar Congo ta rage kiddidigar mutanen da cutar ta halaka, daga 27 zuwa 22, koda yake kuma ana tunani mace macen zai karu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG