Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa Sun Bindige Mutum Takwas Har Lahira a Brazil

Wani dalibi da aka jikkata a harin da aka kai a Brazil. Ranar 13 ga watan Maris 2019.

Gabanin su kutsa cikin makarantar, maharan wadanda aka ce shekarunsu 17 ne da 25, sun kashe wani mai sayar da tsoffin motoci, suka saci mota kafin su kai hari a makarantar.

Wasu tsoffin dalibai biyu, wadanda suka rufe fuskokinsu, sun kutsa cikin wata makaranta da ke Sao Paulo a Brazil dauke da muggan makamai, inda suka bindige mutane, sannan suka kashe kansu daga baya.

‘Yan sanda a yankin da ake kira Suzano, sun ce dalibai takwas sun mutu, sannan wasu 17 sun jikkata.

Gabanin su kutsa cikin makarantar, maharan wadanda aka ce shekarunsu 17 ne da 25, sun kashe wani mai sayar da tsoffin motoci, suka saci mota kafin su kai hari a makarantar.

Wani rahoto ya bayyana cewa mai sayar da motocin kawun daya daga cikin maharan ne.

Wani dan sandan yankin ya ce matasan sun kai harin ne da bindigogi da wukake da adduna da kuma kwari da baka na zamani.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG