Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matatun Mai A Warri Da Fatkwal Sun Fara Aiki.


Matatar Mai.

Matatun mai guda biyun zasu samar da mai kusan lita milyan tara ako wace rana.

Kamfanin NNNPC ya bada sanarwar cewa matatun man fetur na kasar a Fatakwal da kuma Warri a jahar Delta sun fara aiki.

Wannan ya biyo bayan wa'adi d a sabuwar gwamnatin tarayya ta APC karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta baiwa kamfanin na ganin ya sa matatun man sun fara aiki.

Matatar Mai dake Fatakwal ta fara tace danyen man fetur ganga dubu 210 ako wace rana. Wannan kashi 80 cikin dari na karfin matatar ne. Kuma tana samar da lita milyan 5 ko wace rana.

Ita kuma takwararta dake Warri, tana sarrafa gangunan danyen mai dubu 125, wanda yake samarda lita fiye da milyan uku ako wace rana.

Idan matatun man fetur duka hudu da suke kasar suna aiki zasu samar da kasa da lita milyan 20 ako wace rana, fiye da abunda 'yan Najeriya suke bukata ako wani yini.

Ga karin bayani.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG