Accessibility links

Wasu Muggan Macizai Sun Addabi Mutanen Garin Duguri A Jihar Bauchi


Wani mai wasan maciji mai suna Machingaifa rike da wata Mesa wadda ba ta da guba a Afirka ta Kudu.

Mutane akalla 30 sun mutu, wasu da dama sun samu nakkasa, a sanadin wadannan macizai da suka mamaye garin a bayan wata ambaliyar ruwa a shekarar bara

Wasu jinsunan macizai da suka bazu suka yadu a garin Duguri a Jihar Bauchi, sun kashe mutane akalla 30, wasu mutanen da yawa kuma suka jikkata ko suka samu nakasa, tun daga wata ambaliyar ruwa da aka yi a shekarar da ta shige.

Wakilin Sashen Hausa, Abdulwahab Muhammad, wanda yayi tattaki zuwa garin dake kusa da dajin shakatawa na Yankari, ya ga yara kanana da manya da yawa wadanda suka jikkata a sanadin cizon irin wadannan macizan da mutanen garin suka ce ba su taba ganin irinsu ba.

Shugabanni a garin na Duguri sun ce an mika samfurin irin wadannan macizai ga hukumomin kiwon lafiya domin a yi kokarin samo maganin kashe dafin da suke da shi.

Mutanen garin Duguri suka ce jikin mutumin da irin wadannan macizai suka sara yana fitar da jini ta ramukan gashi na hannu da sauran sassan jiki, kuma a yawancin lokuta cikin kasa da minti 30 ya kan zamo ajali. Wadanda suka samu rayuwa kuma, sukan yi hasarar gabobin da wannan maciji ya sara.

Abdulwahab ya tattauna da wadanda suka gamu da wannan hatsarin a garin Duguri, tare da shugabannin al'umma, ya aiko da wannan rahoton.

XS
SM
MD
LG