Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WASU MUTANE A CIKIN UNGUWAR JIDDARI POLO A GARIN MAIDUGURI SUN FARA WATSEWA DAGA UNGUWAR.


Sojoji gaban motar da ta dauko 'yan gudun hijira a Kamaru

Mazauna unguwar jiddaro polo dake cikin garin Maiduguri sun fara tserewa suna barin unguwar domin tsoron kar a sake kai musu hari.

A cikin yan kwanaki biyun da suka gabata ne wasu mahara suka shiga cikin unguwannin Maiduguri, inda suka tada Boma-Bomai kuma suka harbe wasu a cikin gidajen su.

Wannan unguwar ta Jiddari polo na cikin Unguwannin da wadannan maharan suka samu kutsawa suka kai hari, ta tada boma-bomai da kona wasu gidaje a cikin unguwan.

Mazauna unguwar suka ce maharan sunyi nasarar haka ne sakamakon rashin jamian tsaro ta inda maharan suka shigo.

Tun daga wannan harin na baya-bayan nan ne mazauna unguwar suka fara tattara yanasu yanasu suna ficewa daga unguwar, musammam da suka ce suna ganin wasu bakin huskoki masu anfani da baburan da aka hana anfani dasu a jihar tun shekaru2 da suka gabata.

Wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda da ya ziyarci unguwar yace ya gane wa idanun sa yadda mazauna wannan unguwwar ke kwasan kayan su cikin motar nan da ake kira akori kura, domin kokarin ficewa daga cikin wannan unguwa.

Gama abinda daya daga cikin ire-irenwadannan mutanen suka shaidawa Harunan sailin da ya tambaye shi ko ina zashi?

“Zan yi kaura nan unguwar ba dadi zan koma unguwar Bolori, kaya na nan dana yara na harda tsuntsaye na wato kaji, wannan rikicin ne ya tsoratar dani”.

Shima wannan dan talikin ga abinda yake cewa.

‘’Wannan unguwar ita ce hanyar zuwa sanbisa kai tsaye kuma babu jamiin tsaro, kamata yayi ace an girke muna jamian tsaro a wannan wurin nan ba wani jamiin tsaro muna gani akazo aka harbe mutane daya bayan daya kuma aka tafi da motoci, kuma wadanda suka ga dama suka zaba sai sun ace wa mutane ina Buratan naku da Buhari suzo su kwace ku idan sun isa.Muna kallo suka kwashi kayan shaguna suka zuba cikin mota suka tafi.’’

Shima wannan bawan ALLAH da yace shi maaikacin gwamnati shiko cewa yayi.

‘’Ka ganni nan ba unguwar ba garin ma gaba daya zan bari ni maaikacin gwamnati ne, duk wadannan motocin da kake gani wucewa zasu yi wannan wurin ba zai zaunu ba, muna kusa da cikin gari amma hanya ce sambai zuwa Sambisa kowa na barin wurin’’.

Yawancin wadanda Harunan ya zanta dasu sun koka akan rashin jamiaan tsaro a yankin nasu wasu suka ce dan dama-dama idan da akwai jamian tsaro to sun iya zama domin kafin yan boko haram su kawo gare su sun gudu cikin gari.

Wannandai na faruwa ne a dai-dai lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa sojoji kasar waadin kawo karshen boko haram a karshen wannan shekarar.

Ga Haruna Dauda Biu da Cikkakken bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG