Accessibility links

Wasu Mutane Biyu Sunyi Sojan Gona Da Sunan Gwamnan Jihar Bauchi


Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi, tayi nasarar cafke wasu mutane biyu 'yan damfara, da kuma yin karya da cewa dayansu shine gwamnan jihar Bauchi, wato Senata Bala Abdulkadir Muhammed, dayan kuwa shine mataimakinsa, wato P A. Sunyi wannan karya ne a inda suka yi ta damfarar mutane cewa zasu taimaka musu samun kujerar alfarma na aikin Hajji.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Habu Sani Ahmadu, ya shaida wa ‘yan jarida cewar sun samu nasarar kama wadannan mutanen guda biyo ne, bayan rahoton asiri da suka samu.

Daga bisani wakilin muryar Amurka Abdulwahab Muhammad, ya samu damar jin tabakin mutanen biyu da aka kama, wanda ke karyara zama mataimakin gwamnan PA, yayi bayanin yadda abun yafara, da wani Bafulatani wanda yazo mishi da kudi domin neman taimakon samun alfarmar kujerar aikin Hajji.

Yanzu dai ana jiran jin abun da gwamnan ainihi Senata Bala Abdulkadir Muhammad (Kauran Bauchi), zai ce kan wannan batu da wasu sukayi sojan gona da sunansa.

A saurari rahoto daga wakilin Muryar Amurka Muhammad Abdulwahab.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00

Facebook Forum

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG