Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki da Boko Haram Ba Domin Kashe Mutane Ba Ne-Mansur Dan Ali


Janar Mansur Dan Ali, Ministan Tsaron Najeriya
Janar Mansur Dan Ali, Ministan Tsaron Najeriya

A cikin tattaunawar da ya yi da Muryar Amurka minstan tsaron Najeriya ya bayyana manufar yakin da su keyi da Boko Haram inda ya karyata zargin cewa sojojin Najeriya na yiwa mutane kisan kiyashi

Da yake magana ministan tsaron Najeriya Janar Mansur Dan Ali yace kasar Amurka tana ganin ita ce take yin abubuwa daidai bata kula da banbancin yanayi da na tsari daga wannan kasa zuwa waccan.

Ya bada misali da 'yan ta'adan Boko Hamar da kan shiga gari su kashe mutane da dabbobi lamarin da yace karya hakkin bil Adam ne mafi muni. Yace sun yiwa mahukuntan Amurka bayani kan banbancin suke dashi.

Janar Dan Ali yace sojojin Najeriya nada kai'dojin da aka basu kafin su harbi mutum amma su 'ya Boko Haram basu da ka'idoji dalili ke nan da yasa suke kashe mutane da manyan bindigogi. Saboda bin dokar kasa da kasa dangane da yaki, Najeriya tana anfani da karfi iya gwargwado.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG