Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Shugabannin ECOWAS Zasu Burkina Faso da Zummar Warware Rikicin Kasar


Shugabannin ECOWAS a Taronsu a Abuja, Satumba 22, 2015.

Shugabannin kasashe hudu dake cikin kungiyar ECOWAS zasu yi tattaki zuwa Burkina Faso da zummar warware rikicin siyasar da kasar ta shiga bayan juyin mulkinn soja da aka yi cikin makon jiya.

A maraicen jiya Talata ce ake sa ran shugabannin kasashen Senegal, da Togo, da Benin da kuma Najeriya suka yi balaguro zuwa Ouagadougou domin shawarwari na maida mulki hanun farar hula da sojojin tsaro a fadar shugaban kasa suka ayyana.

Madugun sojojin da suka yi juyin mulkin Janar Gilbert Diendere yace zai mika mulki da zarar kungiyar ECOWAS ta bukaci yayi haka, wadanda shugabannin kasashe da suke cikin kungiyar suka yi taro tunda farko a Abujan Najeriya jiya Talata.

Jakadan Faransa Gilles Thibault ya fada ta shafin Twitter cewa an sako shugaban Burkina na wucin gadi Michael Kafando.

Ahalinda ake ciki kuma, Ma’aikkatar Harkokin Wajen Amurka ta shawarci Amurkawa dake Burkina Faso su bar kasar, saboda wasu dalilan tsaro da basu fayyace ba. Ta kuma shawarci Amurkawa kada suyi balaguro zuwa kasar.

Ana zaman dar dar a birnin Ouagadougou tun bayan da sojojin kasar suka fantsama cikin birnin suka ce suna shirin sarandar sojojin da suka ayyana juyin mulkin.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG