Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sun Jikkata a Harin Da Aka Kai Garin Jiddah Na Saudiyya


Garin Jiddah
Garin Jiddah

Akalla mutane uku sun ji rauni ranar Laraba lokacin da wani bam ya tashi a wurin bikin tunawa da ranar tsoffin sojoji da ‘yan kasashen waje suka halarta a makabartar da ba ta musulmi ba a garin Jiddah na Saudiyya, a cewar wata sanarwar da hukumomi suka fitar.

Bam din da aka ‘dana ya tashi ne yayin da karamin jakadan Faransa ya kammala jawabinsa a wurin bikin cika shekaru 102 da kawo karshen yakin duniya na daya. An killace yankin kuma an toshe hanyoyin shiga makabartar bayan harin. Hukumomin Saudiyya na binciken harin.

Kafar yada labaran Saudiyya ta ruwaito cewa wani ma'aikacin karamin ofishin jakadancin Girka da wani mai tsaron Saudiyya ne daga cikin wadanda suka jikkata. Gwamnatin Burtaniya ta ce daya daga cikin ‘yan kasarta shi ne mutum na uku da ya ji rauni. Dukansu ukun an ce sun sami kananan rauni.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa, ofisoshin jakadancin Faransa, Amurka, Ingila, Italia da Girka sun la’anci harin, suna mai cewa “abin kunya ne kuma ba tare da wata hujja ba.”

Faransa, wacce ta ga hare-hare da yawa a cikin makonnin nan, ta kuma yi kira ga hukumomin Saudiyya da su binciki harin kuma a “farauto wadanda suka aikata hakan.”

A watan da ya gabata, wani lamarin da ya faru na kai hari da wuka a karamin ofishin jakadancin Faransa da ke Jiddah, ya bar wani mai gadi da rauni. An kama wanda ake zargin, mutumin Saudiyya ne. Faransa ta sha fama da hare-hare biyu daban-daban a cikin watan Oktoba daga Musulmi ‘yan asalin kasashen waje wadanda suka yi sanadiyyar sare kan wani malami a Paris tare da kashe mutane uku a wata coci a Nice.

Babu tabbas ko harin na Laraba ko an kaishi da niyyar auna jami'an Faransa ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG