Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan APC Na Neman Ficewa Sakamakon Korafe-Korafe Da Suka Biyo Bayan Zabukan Shugabanin Jam’iyyar


Kwamitin sulhu da jam'iyyar APC ta kafa.
Kwamitin sulhu da jam'iyyar APC ta kafa.

Watanni uku kenan da jam'iyyar APC ta kafa kwamitin sulhunta 'ya'yan jam'iyyar masu korafi kan batutuwa daban-daban.

Shugaban Kwamitin Sanata Abdullahi Adamu ya ce lallai haka tana cimma ruwa saboda nasarorin da suke samu wajen sulhunta 'ya'yan jamiyyar a jihohin da suka ziyarta ya zuwa yanzu.

Sai dai wasu na ganin cewa da sauran rina a kaba.

Jam'iyyar APC ta yi ta ninkaya a rikice-rikice wadanda suka jefa makomarta cikin rashin tabbas, bayan da jam'iyyar ta sanar da watan Febrairu na wannan shekara a matsayin watan da za ta gudanar da taron ta na kasa.

Wani abu da ya dauki hankali shi ne, jam'iyyar ta kafa kwamitin sulhu tun watnani 3 da suke wuce, wanda zai yi kokarin dawo da 'ya'yanta da suke neman ficewa saboda wasu korafe-korafe da suka biyo bayan zabukan shugabanin Jam'iyyar daga gundumomi zuwa Jihohi kafin taron kasa da za su yi.

Akan haka Shugaban Kwamitin Sulhu, Sanata Abdullahi Adamu ya ce kwamitin sa yana aiki tukuru wajen hada kan 'ya'yan ta.

Sai dai duk da kokarin ka kwamitin sulhu ya ce yana yi kwararru a fanin zamantakewan dan adam irin su Dr. Farouk Bibi Farouk suna ganin da sauran rina a kaba.

Abin jira a gani shi ne yadda wannan kwamiti zai kammala aikinsa a cikin lokaci saboda jam'iyyar ta samu hadin kan 'ya'yanta wuri guda a lokacin taron kasa da za ta yi domin fitar musu da shugabanni.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG