Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Kai Hare-Hare Kasuwar Dabbobin Potiskum


Dead cows lie amid burned posts Thursday, May 3, 2012 following a raid by gunmen in a cattle market in Potiskum, Nigeria. At least 34 people were killed after a failed cattle raid on Wednesday in a northeast Nigeria market sparked a retaliatory attack by

Rahotannin dake fitowa daga jihar Yobe Arewa maso gabashin Nigeria na cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hare-haren da suka tada gobara a kasuwar dabbobin Potiskum daren jiya laraba, sannan mutane akalla 34 suka kone.

Hare-haren kasuwar shanun ta jikkata mutane sama da ashirin, an kashe dabbobi masu tarin yawa, an kuma sace da yawa daga cikin shanun dake kasuwar.Shaidun gani da ido sun bayyana cewar kafin kai hare-haren tada gobarar, wasu gaggan barayin dabbobi sun shiga kasuwar inda suka rika yiwa ‘yan tireda fashi. An kama guda daga cikin ‘yan fashin lokacin da ya nemi ya tsere, bayan an kamashi ‘yan kasuwar suka kona shi yam utu har lahira. Daga bisani ne kuma sai ‘yan bindigar suka je zagaye na biyu suka rika harbin kan mai uwa da wabi suna kuma jejjefa harsasan dake tada gobara.

Dubi ra’ayoyi (5)

An rufe wannan dandalin

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG