Accessibility links

Sojojin Nijeriya sun kai samame a wata mabuyar 'yan bindiga

  • Ibrahim Garba

'Yan'uwan wasu daga cikin wadanda 'yan ta'adda su ka kashe a yayin da su ke ibada a Kano.

Jami’an tsaron Nijeriya sun kashe wani da ake zargin sa da kasancewa

Jami’an tsaron Nijeriya sun kashe wani da ake zargin sa da kasancewa dan gwagwarmaya da makami na Islama, a yayin da su ke farautar wadanda su ka kai hari kan Kiristan da ke ibada ranar Lahadi.

Jami’ai sun ce wasu jami’an tsaro sun kai samame a wata mabuya da safiyar yau Talata a birnin Kano na arewacin Nijeriya. Sojoji sun kashe mutum guda su ka kama mata uku, a yayin da kuma wani mutum guda ya gudu. Sojojin sun kuma sami makamai da bama-bamai a wurin.

Ranar Lahadi wasu ‘yan bindiga sun hallaka akalla mutane 15 a wani harin da su ka kai a wani dandalin taro na Jami’ar Bayero da Kirista kan yi ibadarsu a wurin.

A wani jawabi a yau Talata, Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, ta bayyana damuwar Amurka game da hare-haren da ake kaiwa kan Majami’u, da gidajen yada labarai da kuma madafun ikon gwamnati a Nijeriya.

Clinton ta ce Amurka na mai Allah wadai da kokarin haddasa tashin hankali tsakanin Kirista da Musulmi a Nijeriya , amman Amurka na tare da duk masu amincewa kasancewar Nijeriya kasar da ta kunshi kabilu da mabiya addinai dabam-dabam a matsayin kinshikin kasar.

Babu kungiyar da ta dau alhakin kai harin ranar Lahadi, wanda ya yi kama da irin hare-haren da kungiyar mayakan sa kan Islama ta Boko Haram ta yi ta kaiwa.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG