Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Maiduguri


Da yammacin yau Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari unguwar Jiddari Polo dake wajen birnin Maiduguri, inda akayi ta jin ‘karan harbe-harbe da fashewar ababen fashewa.

Wakilinmu Haruna Dauda ya je ya ganewa idanunsa inda ya bayyana cewa da misalin 5 da wasu 'yan mintuna na yamma, wasu da ake zaton yaran kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a unguwar Jiddari Polo da ke wajen garin Maiduguri da kuma bayan High Court. Wannan ya tilastawa mazauna unguwar ficewa zuwa cikin gari.

An ce an karan abubuwa masu fashewa masu karfin gaske da kuma harbe-harben bindigogi a unguwannin.

Abun da ke daurewa jama'a kai shine yadda a lokutta da dama ana samun hare-haren da ake zaton cewa yaran 'yan kungiyar Boko Haram ne ke kai hari a bangaren Jidari Polo da High Court.

Saurari Cikakken Bayanin Haruna Dauda Biu

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG