Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Kason Koutoukale Dake Nijar


Niger Attack
Niger Attack

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar mujawu ne sun kai hari a gidan kason dake Kututukale dake cikin jihar Tillaberi a jamhuriyar Nijar

Harin na gidan kason Koutoukale mai tazarar kilomita sittin daga birnin Yamai ya faru ne tsakiyar daren jiya zuwa yau da safe inda aka shafe lokaci ana musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindigan.

Baicin bindigogi da maharan ke tafe dasu har da ma bamabamai lamarin da ya nuna sun shirya harin ta'adanci ne saboda shi gidan kason shi ne wanda aka fi ba tsaro a kasar ta Nijar domin nan ne ake tsare 'yanta'adan da suka shiga hannun hukumomi.

Gwamnan jihar Tillaberi, Muhammad Shalutan da ya je gidan kason yayiwa Muryar Amurka karin bayani. Ya godewa Allah da jami'an tsaro. Jami'an tsaro sun fatattaki maharan har sun kashe daya cikinsu sauran kuma sun afka daji sun yi ta kare. Basu sami abun da suke nema ba. Basu shiga gidan kason ba kuma babu dan kaso daya da ya gudu.

Gwamna Shalutan yace bai san ko maharan guda nawa ba ne amma an ga fankon harsashai da aka harba a harabar gidan kason.

Wannan harin ya zo ne bayan kwana ukku da kungiyar mujawu ta sace wani Ba'amarike a garin Talabak dake jihar Tawa bayan sun kashe wani maigadi da wani jami'in tsaro. Tun kafin wannan ta'asar ma 'yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 22 a sansanin 'yan gudun hijiran Mali dake jihar Tawan.

Wasu 'yan Nijar na ganin dole ne kasashen Nijar, Nigeria, Mali, Chadi da dai sauransu su hada karfi da karfe su bi 'yan ta'adan har cikin Mali.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG