Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Ma'aikatan Man Fetur a Libya


Firayim Ministan Libya Abdullah al-Thinni

An kashe ma'aikatan man fetur goma sha biyu a Libya da suka hada da 'yan kasashen waje hudu

A Libya wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kai hari akan wata rijiyar mai ranar Talata inda suka kashe mutane 12, hudu daga cikinsu ma’aikata ne daga kasashen waje.

Jiya Laraba jami’an kasar suka kara haske akan ‘yan kasashen wajen da suka rasa rayukansu. Biyu dga cikinsu ‘yan kasar Philippines ne sauran biyun kuma daga kasar Ghana suka fito

Jami’an sun kara da cewa wasu cikin wadanda aka kashe an harbesu ne wasu kuma yankan rago aka yi masu.

Rijiyar man dake al-Mabruk tana da tazarar kilomita 160 daga Birnin Sirte wanda yake gabar tekun Mediterranian. Kamfanin Total na kasar Fransa ya mallaki rijiyar kodayake wani kamfanin kasar Libya ne yake gudanar da aiki a wurin.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Kasar ta Libya ta shiga cikin yamutsi tun lokacin da aka hambarar da shugabanta da yayi mata mulkin kama karya Moammar Gadhafi wanda aka kasheshi a shekarar 2011.

‘Yan tawaye masu kishin addinin Islama sun cafke babban Birnin kasar Tripoli inda suka kafa tasu gwamnatin lamarin da ya sa alatilas gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita ta kwashe nata-i-nata ta nufi gabashin kasar.

Kungiyoyin mayaka daban daban suna fafitikar samun iko akan biranen dake da tashoshin jiragen ruwa dake fitar da man fetur zuwa kasashen waje.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG