Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 17 A Sudan Ta Kudu


Wasu ‘yan bindiga da ake zaton sun fito ne daga yankin ma’aikatun gwamnati na Greter Pibor a Sudan ta Kudu, sun kai samame da safiyar ranar Litinin a wani kauyen da ke lardin Bor, inda suka kashe akalla mutum 17 a cewar shaidun gani da ido da kuma hukumomi, hari na baya bayan na cikin jerin munanan rikicin unguwanni a fadin yankin.

Chuti Maker mai shekaru takwas, da ke samun lafiya a asibitin jihar Bor, daga raunin yankar wuka a baya da kirjin sa, ya ce wasu mutane masu yawa sanye da rigunan sojoji da makamai sun kai samame a kauyen Makol-cuei shekaran jiya Litinin da rana.

Chuti ya ce sun fara harbin kan mai uwa da wabi kana suka cinnawa gidaje wuta. Nan ne muka fara gudu su kuma suka bi mu. Sun daba min wuka a bayana na fadi kasa sun kara daba min wuka a kirjina.

Ya ce gardama ta kaure tsakanin mutum biyu cewa su harbe ni, amma sai suka kyale ni, kamar yadda ya fadawa shirin South Sudan in Focus.

Akur Aleng mai shekaru 27 da ta karye a kafa a lokacin harin, ta ce maharan sun kashe mahaifin mijinta kana suka sace jinjirinta mai watanni 14.

Wasu jami’an tsaro ‘yan kalilan da wasu matasan yankin sun fara farautar maharan, inji mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Jonglei Manjo Daniel Tuor.

Ministan Harkokin Cikin Gida a Sudan, Al Tirefi lddris, ya fada a jiya Litinin a birnin Khartoum cewa gwamnati zata tura rundunar tsaro ta hadin gwiwar sojojin da ‘yan sandan Sudan da kananan sojoji domin taimakawa yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG