Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'yan Bindiga Sun Kashe Wani Dan Majalisar Jihar Bauchi a Dass


Shugaban Yan Saandan Nigeria, Muhammaed Adamu Abubakar

Da sanyin safiyar yau Jumma’a ne Jihar Bauchi dake yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta tashi da mummunar labarin mutuwar Dan Majalisar Jihar ta Bauchi, Alhaji Musa Mante Baraza mai wakiltar mazabar hukumar Dass a sandiyyar harbi da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka mai a cikin gidansa dake garin Dass da misalign karfe daya (1:00am) na daren jiya wayewar garin yau Jumma’a.

‘yan bindigar, sunyi garkuwa da matansa biyu Rashida Musa Mantai mai shekaru 40 da haihuwa da kuma Rahina Musa Mante mai shekaru 35, sai ‘yarsa Hafsa mai shekara daya da haihuwa.

Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Bauchi, Abdulwahab Muhammad ya zanta da kakkakin rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi DSP Muhammad Wakil ta wayar taraho inda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kuma shaida mai cewa duk da cewa har yanzu ba a gano wadanda suka aikata wannan laika-aikar ba, jami’an ‘yan sanda suna ci gaba da bincike domin gano wadanda suka aikita wannan laifi domin a mika su ga kotu.

A nasa bangaren kuma, Jami’in yada labarai na masarautar Dass, Bala Muhammad Nalado, ya shaida wa wakilin namu cewa a lokacin da ‘yan bindigar suka kai wannan farmaki babu jami’an tsaro tare da marigayin.

Ya kara da masa bayanin cewa, marigayin yana raba kafa wajen kwanan tsakanin Bauchi da Dass.

Bayannan Nalado sun nuna cewa mai martaba sarkin Dass bai ji dadin lamarin ba, kuma yayi kira ga jami’an tsaro su tabbatar sun zakulo wadanda su ka yi wannan aika-aikar.

Kazalika, gwamnatin Bauchi da majalisar Jihar sun bayyana kisan dan majalisar a matsayin ta’addanci tare da alkawarin zakulo duk wadanda suka yi wannan aika-aikar.

Ga wakilinmu a Bauchi, Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00


Facebook Forum

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG