Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Turawa Shida a Gabar Tekun Najeriya dake Yankin Niger Delta


'Ya Tsagerun Niger Delta

Garkuwa da mutane a yankin Niger Delta ba wani abu ba ne sabo saboda ko kafin wadannan shidan da aka sace, wasu ‘yan bindiga sun sace wasu likitocihudu a yankin kuma har yanzu ba’a san inda suke ba

Wasu ‘yan bindiga a gabar ruwan Najeriya a yankin Niger Delta sun yi garkuwa da wasu turawa shida tare da karkata jirginsu zuwa wani wuri daban.

Cikin wadanda aka sacen, hudu ‘yan kasar Philippines ne yayinda sauran biyu sun fito ne daga kasashen Ukraine da Hungary, kamar yadda ofisoshin jakadancin kasashen suka sanar.

Ya zuwa yanzu dai babu wata hanyar tuntubar ‘yan bindigan domin sun kai jirgin wani wuri da ba’a tantance ba tare da sauran ma’aikatan jirgin su 12.

DSP Imoni Monday, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Rivers, ya ce basu da masaniya akan lamarin amma yi alkawarin ba da bayani da zara ya samu wani abu.

A halin yanzu kuma, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta, Andrew Onyemeka, yace sun kama wasu mutane akan sace likitoci hudu da ya faru tun farko kuma sojojin ruwa da na sama suna aiki kafada da kafada domin gano mutanen.

Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG