Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kai Hari Garin Shawu Dake Jihar Adamawa


Wasu 'yan kunar bakin wake da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne yi kokarin kai hari a wani Cocin Katolika dake burnin Shawu, dake jihar Adamawa.

Kamar yadda rahotanni da kuma mazauna yankin ke cewa wasu 'yan kunar bakin wake ne da ake zargin 'yan Boko Haram ne, suka yi shigar burtu da zimmar shiga cocin katolika dake garin na Shuwa, to sai dai kuma kafin su karasa cikin cocin sai damarar bom dake jikinsu ya tashi wanda nan take kuma biyu suka mutu yayin da aka ce na ukunsu ya ranta ya na kare, kamar yadda wani dan sakai ayankin ya tabbatar wa wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'ziz ta waya.

Kawo yanzu rundunar 'yan sandan jihar Adamawan ba ta yi karin haske ba kan lamarin, to sai dai kuma kakakin rundunar tsaron farin kaya ta sibil defense a jihar Adamawan Suleiman Baba ya yi karin haske game da abun da ya faru da kuma halin da ake ciki.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da hada hancin sakamakon zaben gwamna da kuma na 'yan majalisar dokokin da aka kada jiya asabar, wanda tuni aka fara kawo sakamakon kananan hukumomi zuwa shedikwatar hukumar zabe dake fadar jihar.

To sai dai yayin da ake jiran bayyana sakamakon a hukumance, tuni wasu kusoshin jam’iyar APC dake mulki a jihar Adamawa suka bayyana farin cikinsu da yadda zaben ya gudana cikin lumana. Dr Mahmdu Halilu Ahmad wanda da shi aka fafata a zaben fidda gwani na jam’iyar yace akwai abun lura game da zaben na jihar Adamawa.

Saurari cikakken rohoton Ibrahim Abdul'aziz daga Yola.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG