Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'yan sanda sun shiga tsaka-mai-wuya a Gombe


'Yan sanda ke nan suna samar da tsaro a wajen wani taron gangamin siyasa a watan Nuwamba 2014.

Wasu 'yan sanda guda biyu sun fada hannun hukuma domin ana kyautata zato su ne suka harbe wani saurayi a Gombe.

Lukuman Muhammad Jibrin shi ne saurayin da ake zargin 'yan sandan da harbewa a garin Gombe.

Da farko yayin da lamarin ya faru an ce hadarin mota ne dan saurayin ya yi ya mutu.To amma lokacin da aka je asibiti daukar gawarsa domin a yi masa jana'iza sai aka ga alamun harbi a jikinsa.

Dan uwan mamacin ya yi karin haske bisa abun da ya faru. Ya ce da daddare bayan karfe goma aka kira shi aka ce Allah ya yiwa Lukman rasuwa sanadiyar hadarin mota.

To amma da suka je wajen wanka sai aka ga harbi a jikinsa. Nan take aka tsayar da shirin jana'izarsa. Hatta kwamishanan 'yan sandan jihar ya ce bai yadda hadari ne saurayin ya yi ba.

Yanzu dai an kama 'yan sanda biyu. Shi ma DPOn wurin ya fada cewa ya ga ramin da harsashen 'yan sandan ya huda a motar ya kuma sami saurayin ya kasheshi.

Ga karin bayani a wannan rahoto

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG