Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Yankuna Su Na Da Wahalar Zuwa, In Ji Likitocin Ba Da Agaji


Wasu ma'aikatan lafiya suna kula da marasa lafiya

Matsalar yunwa ga yara kanana ko kuma tamowa, matsala ce da ta addabi masu gudun hijra da suka fice daga gidajensu sanadiyar rikicin Boko Haram da ya daidaita wasu al'umomin jihar Borno, da ma wasu sassan kasashe da ke makwabtaka da Najeriya.

Wannan matsala dai ta ja hankulan duniya, tun bayan da hukumar da ke kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan halin da 'yan gudun hijra ke ciki.

Hukumar ta ce idan ba a yi hattara ba sama da yara dubu 50 za su mutu nan da karshen shekarar nan saboda matsalar yunwa.

Rikicin na Boko Haram ya raba akalla mutane miliyan biyu da muhallansu a jihar da wasu yankunan kasashe da ke makwabta da Najeirya.

Kuma bayanai sun yi nuni da cewa kashi 90 na mutanen da aka raba da muhallan nasu sun bazu a cikin birnin Maiduguri, yayin da kashi goma ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijra da aka samar.

A baya, an yi zargin cewa wasu suna sace abincin da ake samarwa domin 'yan gudun hijrar, lamarin da ya sa masu gudun hijrar suka yi zanga zangar lumana a makawnanin baya a binrin Maiduguri.

Domin jin halin da 'yan gudun hijrar ke ciki da irin kalubalen da ake fuskanta wajen kyautata rayuwarsu, saurari hirar wakilin Sashen Hausa na Murayar Amurka, Haruna Dauda da wani jami'in kungiyar likitoci ta kasa da kasa, wato Doctors Without Border, Dr. Issiaka Abdou:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00

XS
SM
MD
LG