Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata ba-Yazidiya Da Wani Baki Sun Ci Lambar Yabo ta Nobel


Nadia Murad da Dokta Denis Mukwege
Nadia Murad da Dokta Denis Mukwege

A wani cigaba ga tsirarun jinsi a fadin duniya, wata 'yar kabilar Yazidi da kuma wani bakar fata sun ci lambar yabo ta zaman lafiya ta Noble. Duk da ya ke ba wannan ne karon farko da tsirarun jinsi su ka ci wannan lambar yabo ta Nobel ba, wannan zai kara masu kwarin gwiwa.

An ba da Lambar Yabo ta Nobel ta zaman lafiya ma Nadia Murad, wata 'yar kabilar Yazidi kuma 'yar gwagwarmayar rajin kare hakkin dan adam, wacce kuma kafin ta tsere ta kasance sadaka lokacin da ta ke hannun kungiyar ISIS a kasar Iraki; sai kuma Dr. Denis Mukwege, likitan mata wanda ke jinyar matan da aka masu fade a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Kwamitin bayar da lambar yabon, wanda mambobinsa 'yan kasar Norway ne, ya fada a wata takardar bayani ta jiya Jumma'a cewa lambar yabon ta na tabbatar da "himmar da mutanen su ka bayar, wajen dakile fade a matsayin wani nau'i na hari a lokacin yaki ko kuma tashin hankali."

Murad, 'yar shekaru 25 da haihuwa, ita ce ta kafa kungiyar da ake kira Nadia Initiative da Turanci, wadda kungiya ce da ta dukufa wajen taimaka ma matan da yaki da sauran masifu su ka rutsa da su.

Sakatare-Janar din Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fada jiya Jumma'a cewa yekuwa mai karfi da kungiyar Murad ta rika yi, ta sosa ran mutane a fadin duniya, sannan ta taka rawa gaya wajen sa Majalisar ta binciki irin azabar da ita Nadia da wasu mata da dama su ka fuskanta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG