Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Cuta Mai Kamar Mura ta Addabi Kasar Saudi Arabia, me Masu Umra Zasu Domin Kare Kansu?


Musulmi da suke aikin hajji ko umra suka sanya kariya daga kamuwa d a cutar mai kama hanyoyin numfashi.
Musulmi da suke aikin hajji ko umra suka sanya kariya daga kamuwa d a cutar mai kama hanyoyin numfashi.

Wannan cuta masana suka ce sakacin hukumomin kasar Saudiyya ce ta sa cutar ta yadu.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya ta ce cutar nan mai kama da mura, wacce ta zaburo cikin watan Afrilu a kasar Saudiyya yanzu ta lafa, duk da haka hukumar tace her yanzu da sauran aiki wajen shawo kan cutar.

Cutar da ake kira MERS a takaice cikin harshen turanci ta kama mutane fiye da 700 a duk fadin duniya dukkansu sun kamu da cutar ta wani dalili mai nasaba da kasar Saudiyya.

Cutar mai shigen mura ta kuma kashe mutane fiye da 250 a fadin duniya.

Wannan cuta tuni ta yadu musamman a kasashe da suke yankin gabas ta tsakiya kamar su Jordan, Iran da Aljeriya, dukkan wadanda suka kamu a da cutar daga wadanan kasashe mutane ne da suka kai ziyara kasar Saudi Arabiya domin ibada.

Ko anan Amurka wasu mutane biyu masu aikin kiwon lafiya a kasar Saudi Arabia wadanda suka dawo nan Amurka sun kamu d a cutar. Mutanen 'yan asalin jihohin Florida da Indiana ne.

Dr. Hassan Bashir Jibrin likita ne mai zaman kansa a jihar Florida dake nan Amurka yayi karin haske dangane da wannan cuta.

Ga Kashi na daya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG