Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren harkokin wajen Amirka yayi watsi da rahotanin dake cewa Amirka ta bata da Saudi Arabiya


Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry,a hagui.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, yayi watsi da rahotanin dake cewa an samu sabanin sosai tsakanin Amirka da kasar Saudi Arabiya.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, yayi watsi da rahotanin dake cewa akwai sabanin sosai tsakanin Amirka da kasar Saudi Arabiya.

A bayan da ya gama ganawa da takwaran aikinsa na Saudi Arabiya Saud Al Faisal a birnin Paris a ranar Litinin, jiya Talata Mr Kerry yace ya tabbata ra'ayinsu yazo daya.
Mr Kerry yace Amirka zata ci gaba da tuntunbar kasar Saudi Arabiya kamar yadda ta saba yi akan batutuwa da dama.

Jami'an kasar Saudi Arabiya suna ta baiyana takaicinsu da fushinsu akan kiyawar da Amirka tayi na kaddamar da hare haren soja akan gwamnatin Syria ta Bashar Al Assad, bayan da aka yi zargin cewa gwamnatin Syrian tayi amfani da makamai masu guba akan farar hula a watan Augusta.

Haka kuma Saudi Arabiya tana nuna damuwa akan alkibilar tattaunwar da ake yi akan makaman nukiliya, da kuma yiwuwar sasantawa tsakanin Amirka da Iran.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG