Accessibility links

Wata Fitacciyar Makarantar Addinin Musulunci A Duniya Ta Goyi Bayan Yaki Da Cutar Polio


Wasu masu aikin rigakafin cutar polio

Makarantar Islama ta kasa da kasa da ake kira International Islamic Fiqh Academy, ta bayyana goyon bayan rigakafin cutar shan inna da ake yi a Najeriya tare da jadada cewa zata yiwa dukan wanda ya kaiwa masu aikin rigakafin hari fatwa.

Makarantar Islama ta kasa da kasa da ake kira International Islamic Fiqh Academy, ta bayyana goyon bayan rigakafin cutar shan inna da ake yi a Najeriya tare da jadada cewa zata yiwa dukan wanda ya kaiwa masu aikin rigakafin hari fatwa.

Kungiyar ta kuma yi kira ga iyaye su tabbata an yiwa ‘ya’yansu maza da mata rigakafin cutar ta kuma jadada cewa rigakafin bashi da wata illa. Kungiyar ta kuma kara fadakar da iyaye da cewa, hakin kula da lafiyar ‘ya’yansu ya rataya a wuyansu.

Makarantar wadda ke karkashin kungiyar hadin kan addinin Islama “Organisation of Islamic Cooperation (IOC),” ta bayyana cewa, tana addawa da hare-haren da ake kaiwa masu aikin rigakafin shan inna wadanda suke gudanar da ayyukansu kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Makarantar ta bayyana goyon bayan shirin ne a wani taron malaman Islamiya da aka yi a Al-Azhar Alkahira babban birnin kasar Misira. Kwararru a wajen taron sun tattauna a kan rawar da shugabannin kungiyoyin Musulmi zasu iya takawa da zai taimaki al’ummominsu kare lafiyar dukan ‘ya’yansu.

Mai Martaba Sarkin Musulmi , Alhaji Sa’ad Abubakar III, yana kan gaba a kamfen yaki da shan inna a Najeriya, inda ya rika yin kira ga iyaye su bari a yiwa ‘ya’yansu allurar rigakafi ya kuma jadada cewa bata da illa.

Mai Martaba Sarkin Musulmi ya bayyana cewa an gudanar da bincike a kan allurar rigakafin an kuma tabbatar da sahihancinta. Bisa ga cewarshi, hukumar tantance ingancin magunguna ta kasa -NAFDAC ba zata amince da maganin da yake da illa ba , ta kuma amince da ingancin allurar rigakafin.
XS
SM
MD
LG