Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Jami'ar Hukumar Zaben Kenya Ta Yi Murabus Tare da Arcewa daga Kasar


Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta

Wata wakiliyar hukumar zaben kasar Kenya tayi murabus mako daya kafin a sake zaben shugaban kasa da ake shirin yi, abin da ya kara ruruta wutar rikicin siyasar kasar dake gabashin Africa.

Roselyn Akombe, ta fitar da wata sanarwa daga birnin New York a jiya Laraba, ta na mai cewa "zaben da ake shirin sake yi ranar 26 ga watan Oktoba ba zai cimma mizanin da ake fatan gani ba a zaman sahihin zabe."

Akombe ta fadawa BBC cewa ta gudu daga Kenya ne bayan barazanan da akayi ta yi wa rayuwarta.

Shguaban kasar Kenyar,Uhuru Kenyatta shine ya lashe zaben da akayi na ranar 8 ga watan Agusta, amma kusan wata guda bayan zaben, kotun kolin kasar ta soke sakamakon zaben, saboda hukumar zabe ta tafka kura-kurai. Kundin tsarin mulkin Kenya ya bayar da kwanaki 60 a sake gudanar da zabe bayan soke shi.

Amma kuma sake zaben ya shiga wani hali tun makon da ya gabata, lokacin da ‘dan takarar jam’iyyar adawa Raila Odinga ya cire kansa daga zaben.

Sai dai kuma duk da cewa ya janye kansa a zaben, hukumar zaben kasar ta ce ba za a cire sunan Odinga daga takardun zabe ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG