Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata kotu a Abuja ta ci tarar hafsan hafsoshin sojojin Nigeria Naira miliyan 11


Hafsan Hafsoshin Sojojin Nigeria Janar Tukur Buratai
Hafsan Hafsoshin Sojojin Nigeria Janar Tukur Buratai

Matasa 11 daga garin Shongom a jihar Gombe zasu samu Naira miliyan 11 biyo bayan tarar da wata kotun tarayya dake Abuja ta yiwa hafsan hafsoshin sojojin Nigeria sanadiyar cin zarafin da sojoji suka yi masu

Jaridar Vanguard ta yanar gizo ta jiya Alhamis ta bada rahoton cewa wata kotun tarayyar Nigeria dake Abuja ta ci hafsan hafsoshin sojojin Nigeria Janar Tukur Buratai tarar zunzurutun kudi har Naira miliyan goma sha daya saboda cin zarafin da sojoji suka yiwa wasu matasa 11 a jihar Gombe

Mai shari’a Justice Ijeoma Ojukwu ta ce yadda sojojin Janar Buratai suka kama matasa 11 a Gombe, suka tsare su tun daga ranar 6 ga watan Yulin wannan shekarar, suka ci gaba da gana masu ukuba ba ya cikin tsarin mulki ko dokokin Nigeria.

Jaridar Vanguard ta ce Justice Ijeoma Ojukwu ta ba da umurnin a saki matasan a kuma biya kowannensu diyar Naira miliyan daya.

Maganar ta samo asali ne lokacin da matasan suka samu gawar wani dan uwansu a gonarsu a kauyen Shongom dake jihar Gombe. Sun dauki gawar su kaita gida sai sojoji suka gamu dasu suka kama su. Tun daga lokacin ne, 6 ga watan Yuli suka shiga azabar sojojin kamar yadda jaridar Vanguard ta rubuta

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG